Amincin Allah ya tabbata gareku.
Muna taya masana da manazarta murna waɗanda suka sami nasarar shiga cikin ɗab’in Mujallar BIRAM bugu na uku fita ta farko a watan Yuni shekarar 2025.
Ku shiga https://www.biramjournal.com.ng/current domin sauƙe kwafinku.
Muna fatan Allah ya amfanar da mu ilimin da ke ƙunshe ciki, tare da fatan ci gaba da ba mu shawara da haɗin kai da goyon baya wajen farfaɗo da inganta harkar ilimi.
Mu haɗu a ɗab’i na gaba (Bijochs/Dec, 2025/Vol. 3 – Issue 2)
Muna godiya.
Dr Ginsau Abdulkadir
Sakataren Mujallar Biram
BIRAM BUGU NA UKU FITA TA FARKO

